A cewar shugabar kwamitin zartaswar mambobin nahiyar Afirka na dandalin Elsie Kanza, mahalarta taron za su maida hankali ga zakulo hanyoyin da za su sharewa nahiyar Afirka fage, na rungumar fasahohin wannan karni.
Ta ce yanzu haka akwai kusan mutane biliyan 4 a dukkanin fadin duniya da basu da zarafin amfani da yanar gizo, kuma kashi 90 bisa dari na wannan adadi na zaune ne a kasashe masu tasowa ciki hadda Afirka. Bisa wasu alkaluman kididdiga, al'ummun Afirka na da kaso 28.6 ne kacal na masu amfani da fasahar yanar gizo.
Kanza ta ce bisa tsokacin da kwararru ke yi, hada al'ummun nahiyar da yanar gizo na nufin martaba muhimmancin dake tattare da fasahar sadarwa a rayuwar bil Adama. Masu wannan ra'ayi na ganin hakan zai bunkasa tattalin arzikin nahiyar, ya kuma inganta harkar kiwon lafiya, da ilimi, da kuma samar da karin guraben ayyukan yi.
Za dai a gudanar da taron na bana ne tsakanin ranekun 11 zuwa 13 ga watanan nan na Mayu. Taken sa kuma shi ne "hade albarkatun nahiyar Afirka ta hanyar bunkasa fasahohin sadarwa na zamani". (Saminu)