Haka kuma, bankin duniya ya yi hasashe cewa, karuwar tattalin arziki a yankin Afirka dake kudu da Sahara za ta ci gaba da kasancewa maras karfi. A tsakanin shekarar 2003 da ta 2008, matsakaicin adadin karuwar tattalin arziki a wannan yanki ya kai kashi 6.8 bisa dari, amma a halin yanzu, adadin bai wuce rabin adadin ba.
Bankin duniya ya ce, dalilan da suka haddasa haka a Afirka snna da nasaba da faduwar farashin danyun kayayyaki a kasuwar kasa da kasa, musamman ma man fetur, haka kuma tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba shi ma ya kawo illa kan lamarin.
Bugu da kari, wasu matsaloli kamar su karancin wutar lantarki, tangardar yanayin siyasa, fari da kuma kalubale a fannin tsaro da dai sauransu sun kuma kara janyo illa ga bunkasuwar tattalin arziki a yankin. (Maryam)