Bangarorin biyu sun bayyana cewa, za su ci gaba da nazari kan hanyoyin gudanar da hadin gwiwa a tsakanin Rasha da Amurka, domin karfafa yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar, da tabbatar da taimakon jin kai da za a samar wa al'ummomin kasar, da kuma fara yunkurin siyasa domin warware matsalar da kasar take fuskanta a halin yanzu.
Kaza lika kuma, ministocin biyu sun cimma ra'ayi guda kan ci gaban hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa tsarin tawagar nuna goyon baya ga kasar Syria ta kasa da kasa.
A wani ci gaban kuma, an ce an samu aukuwar hare-hare da dama a wurare daban daban na kasar ta Syria, wadanda suka haddasa a kalla rasuwar mutane 31, yayin da kimanin 122 suka jikkata.
An fara samun kyautatuwar yanayin tsaro a kasar Syria, bayan da kasashen Amurka da Rasha suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakanin bangarori daban daban da rikicin kasar ya shafa. Amma a kwanan baya, an ci gaba da samun tashin hankula a kasar, haka kuma, wasu daga tsagin 'yan adawar kasar sun sanar da janye jikinsu daga yarjejeniyar tsagaita bude wuta, lamarin da ya kawo barazana ga yanayin tsaron kasar ta Syria. (Maryam)