in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya sanar da tura karin sojoji 250 zuwa Syria
2016-04-26 09:45:57 cri
A jiya Litinin 25 ga watan nan ne shugaban Amurka Barack Obama, ya sanar da aikewa da karin sojoji 250 zuwa kasar Syria, domin taimaka wa dakarun gungun 'yan adawa, wajen yaki da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS.

Shugaba Obama, ya sanar da wannan kuduri ne a yayin da yake jawabi a birnin Hanover dake arewacin kasar Jamus. Ya ce, a halin yanzu, kungiyar IS tana ci gaba da haifar da kalubale ga tsaron kasa da kasa, kuma bangarorin da abin ya shafa na samun sakamako da gamsarwa wajen yaki da kungiyar cikin hadin gwiwa, sai dai duk da hakan ana bukatar zage damtse domin cimma cikakkiyar nasara. Hakan ne ma a cewar sa ya sa yake kira ga kasashen Turai, da kuma kasashen dake cikin kawancen tsaro na NATO da su kara ba da gudummawar yaki da kunigyar IS. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China