A wannan rana kuma, kungiyar IS ta fidda wata sanarwa cewa, kungiyar ta harbe wani jirgin saman sojan gwamnatin kasar Syria a yankin karkara dake gabashin babban birnin kasar, Damascus, sa'an nan kuma, kungiyar ta kama matukin jirgin. Amma ba a sami labari game da ikirarin kungiyar ba daga kafofin watsa labarai na gwamnatin Syria ba.
Haka kuma, cikin wata sanarwar da cibiyar hafsoshin sojojin kasar Amurka ta fidda, an ce, bisa binciken da kasar Amurka ta yi dangane da hare-haren sama da aka kai a kasar Syria da Iraq kwanan baya, an gano cewa, hare-haren saman da aka kai sun haddasa rasuwar fararen hula guda 20, yayin da 11 suka jikkata. (Maryam)