Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya tsamo wasu daga bayanan dake cikin wasikar, inda ya ce, kai hare-haren igogi kan wasu unguwannin fararen hura dake birnin Damascus, da Halab a ranar Asabar da ta gabata, ya sabbaba mutuwar mutane 11, tare da raunata wasu 59, ciki har da kananan yara, da mata da tsofaffi, kana hare-haren sun lalata gidaje da makarantu da asibitoci da dama.
Labarin ya kara da cewa, sojojin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin Islama, da sojojin fafutukar neman 'yancin kasar Syria, masu kiran kan su da dakarun 'yan adawa ne suka aikata wannan ta'asa. A cikin wasikar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta jaddada cewa, wadannan hare-hare na ta'addanci ba za su kawar da imanin gwamnatin kasar Syria na yaki da ta'addanci ba, kana ba za su kawo cikas ga gwamnatin kasar wajen kokarin ta na warware batun Syria ta hanyar shawarwari ba. (Zainab)