in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 21 sun mutu a sakamakon fashewar boma-bomai biyu a kudancin kasar Somaliya
2016-02-29 10:38:37 cri
'Yan sandan kasar Somaliya sun bayyana cewa, wata fashewar boma-bomai da ake zaton na kunar bakin wake ne a yankin Baidoa dake kudancin kasar Somaliya, ta haddasa mutuwar mutane a kalla 21 tare da raunata wasu mutanen.

'Yan sandan yankin Baidoa sun bayyana cewa, an samu fashewar bom da aka dasa cikin wata mota a wani otel dake yankin Baidoa, kana wani dan kunar bakin wake ya tada wani bom din dake jikinsa a wani otel na daban dake yankin.

Wadannan hare-haren biyu sun yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 21, yawancinsu su ne fararen hula, ana kuma zaton yawan mutanen da suka mutu ko suka ji rauni a sakamakon hare-haren zai iya karuwa.

Kungiyar Al Shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da daukar alhakin wannan hari. Al Shabaab mai sansani a kasar Somaliya kungiya ce ta masu tsattsauran ra'ayi dake da nasaba da kungiyar Al Qaeda, wadda ke haifar da rikice-rikice da dama a kasar Somaliya, da kasashen dake dab da Somaliya a wadannan shekaru. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China