Shugaba Mohamoud ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taron dandalin harkokin tsaro da aka shirya a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, yanzu haka kasar tana yaki ne da kungiyar Al-Shabaab wadda ta kasance babbar barazanar tsaro ga al'ummar duniya baki daya.
Ya kuma bayyana cewa, nan ba da dadewa ba gwamnati za ta warware jinkirin da aka samu na biyan albashin sojojin kasar, duk da matsalar karancin kudin da gwamnatin ke fama da shi.
Shugaban na Somaliya ya kuma yi maraba da shawarar da majalisar zartarwar kasar ta gabatar a wannan mako game da matakan tsaron da ya kamata a dauka na rage hare-haren da kungiyar Al-Shabaab ke kaddamawar a sassan kasar.
Kalaman shugaban na zuwa ne yayin da kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida ta kara zafafa hare-haren da ta ke a makon da ya gabata, hare-haren da suka yi sanadiyar rayukan mutane da dama, galibinsu fararen hula.(Ibrahim)