Mahukuntan kasar Rwanda sun gayyaci jami'an sanya ido su kimanin 1700, domin ganewa idanun su yadda za ta kaya, a kuri'ar raba gardama da 'yan kasar za su kada, game da yiwuwar kara wa'adin shugabancin kasar bayan zango biyu.
A cewar shugaban hukumar zaben kasar NEC Mr. Kalisa Mbanda, kuri'ar raba gardamar da za a gudanar a ranekun 17 da 18 ga watan nan, za ta lakume kudi har dalar Amurka miliyan 1 da dubu dari 3.
Mr. Mbanda ya kara da cewa ya zuwa yanzu, an kammala kaso 80 cikin dari na shirin kada kuri'ar, kuma masu aikin sa kai 68,000 sun amince su tallafa wajen cimma nasarar aikin.(Saminu Alhassan)