An dai sauyawa 'yan gudun hijirar dake samun mafaka a sansanin Dadaab dake kasar Kenya wurare ne, bayan da su da kan su suka nuna sha'awar hakan.
Har wa yau hukumar ta UNHCR ta ce yanzu haka tana ci gaba da aikin maida karin wasu 'yan gudun hijirar gida ta hanyoyin mota bayan da aka dakatar da hakan tsahon lokaci. Tuni dai aka yi jigilar mutane 1,902 zuwa kasar Somalia ta titin mota dake Dhobley.
Bugu da kari hukumar ta ce za ta ci gaba da safarar wasu karin 'yan gudun hijirar ta jiragen sama zuwa birnin Mogadishu. A kuma halin da ake ciki ofishin dake kula da wannan aiki, karkashin hukumar UNHCR, da takwarar ta ta kasar Kenya ko DRA, tare da tallafin NRC na kasar Norway, na kokarin tallafawa wasu mutanen 1,700 koma wa gida.
Da dama daga 'yan gudun hijirar dai na komawa yankunan su na asali da suka hada da Kismayo, da Mogadishu, da Baidoa da Luuq, wadanda ke kudanci da tsakiyar kasar ta Somalia. (Saminu)