in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta karbi bakuncin wasannin CHAN a shekarar 2018
2016-02-08 13:33:35 cri
Wani kusa a hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta Afrika CHAN ya ce, kasar Kenya za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2018.

Almamy Kabele Camara, shi ne mataimaki na biyu ga shugaban hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta Afrika, ya shedawa 'yan jaridu a Lahadin nan cewar, kasar wacce ke gabashin Afrika za ta fara shirye-shirye domin karbar bakuncin gasar wasannin.

Ya kara da cewar kasar Rwanda ta yi kokari har ma ta samu matsayi na farko a karbar bakuncin gasar wasannin a wannan shekara. Don haka ya bukaci Kenya da ta fara shirye shirye a kan lokaci domin ta samu nasarar karbar bakuncin gasar wasannin a shekarar ta 2018.

Wannan shi ne karo na uku da aka sake dawo da wasannin na CHAN a shiyyar gabashin Afrika, tun bayan wanda kasar Sudan ta karbi bakuncinsa a shekarar 2011.

Camara ya ce, an amince da kasar Kenya ta karbi wasannin ne tun a shekarar da ta gabata, bayan yin la'akari da wasu ka'idoji da ake sa ran kasar za ta cika don karbar bakuncin wasannin wadanda suka hada da samar da muhimman kayayyakin da ake bukata da kuma tsaro.

Da yake karin haske game da shirye-shiryen wasannin CHAN na shekara ta 2016, Camera ya ce kasar Rwanda ta kashe kimanin dalar Amurka miliyan 23 domin karbar bakuncin wasannin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China