Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da yake maganan game da ziyarar da shugaban kasar Nigeriya Muhammadu Buhari ya kai kasar, yace ziyarar ta samar da damar a cigaba da raya huldar hadin gwiwwa wanda ya samu cigaba kwarai.
Shi ma a nashi jawabin Muhammadu Buhari na Nigeriya ya jinjina ma zumuncin dake tsakanin kasar da Kenya.
Shugabannin biyu suka amince da cewar zasu hada hannu tare wajen magance kalubalolin dake fuskantar kasashen su kamar su cin hanci da rashawa, ta'addanci da tsatsauran ra'ayi wanda suke ganin yake kawo cikas na cigaba.
Mr. Kenyatta ya lura cewa Kenya da Nigeriya suna fuskantar matsaloli ta'addanci, tsatsauran ra'ayi na matasa da tsatsauran ra'ayi na tashin hankali, yana mai cewa kasashen biyu don haka zasu yi aiki tare don kawo karshen hakan.
Shugaba Muhammadu Buhari da Uhuru Kenyatta sun kuma amince cewar kasashen biyu zasu tabbatar da yarjeniyoyin hadin gwiwwa da aka saka ma hannu an aiwatar da su yadda ya kamata.