Ya ce a madadinsa da iyalinsa yana mika sakon fatan alheri ga al'ummar kasar Sin, yayin da suke bikin murnar shiga sabuwar shekara a Litinin mai zuwa wato 8 ga watan Fabrairun shekarar 2016.
Ya jaddada cewar dangantakar Sino-Kenya ta shafe shekaru sama da 15, kuma tana nan daram, sannan kasashen biyu na cin moriya.
Mista Kenyatta ya kara da cewa, kasashen Kenya da Sin sun kulla dangantakar kasuwanci tun shekaru aruaru da suka shude. Kuma kasashen biyu suna da alaka ta kut da kut ta fuskar yakar cin zali da mulkin mallaka. A cikin wadannan kwanaki, kasahen na yin hadin gwiwa ne wajen bunkasa ci gaba, da yin aiki tare kan muhimman al'amurran ci gaba.(Ahmad Fagam)