Wasu shugabannin Afrika za su isa Burundi domin shawarwari kan tattaunawar siyasa
Shugaban kasar Senegal Macky Sall da ma sauran shugabannin Afrika za su isa kasar Burundi domin shawarwari tare da gwamnatin Burundi da sauran masu ruwa da tsaki na kasar kan tattaunawar siyasa, da kuma ta wani hali yiyuwar tura wata tawagar Afrika ta rigakafi da bada kariya a kasar Burundi, in ji fadar shugaban kasar Senegal a ranar Litinin. Matakin an dauke shi a yayin babban taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) karo na 26, da ya gudana a ranakun 30 da 31 ga watan Janairu a birnin Addis Abeba na kasar Habasha, a cewar wannan majiya.
Wannan tawaga ta manyan jami'ai za ta hada, baya ga shugaba Macky Sall, da sunan yammacin Afrika, shugabannin Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz, Afrika ta Kudu Jacob Zuma, Gabon Ali Bongo Odima da kuma faraministan Habasha Hailemariam Desalegn, in ji fadar shugaban kasar Senegal. (Maman Ada)