A yayin wannan ziyara da ta soma a ranar Alhamis da yamma, tawagar ta gana da shugaban Burundi Pierre Nkurunziza da mataimakinsa, ministan harkokin waje, wakilan jam'iyyun siyasa, kafofin sadarwa da kungiyoyin fararen hula, da ma shugabannin addinai, in ji MDD a cikin wata sanarwa.
Da yake magana a kafar rediyon MDD bayan ganawa tare da shugaba Nkurunziza, jakadan Angola dake MDD, Ismael Gaspar Martins, dake jagorantar wannan tawaga tare da jakadiyar kasar Amurka Samantha Power da kuma mataimakin jakadan kasar Faransa Alexis Lamek, ya bayyana cewa tawagar ta dubi matsalar tsaro a cikin kasar da kuma shawarar shiga tsakani ta kungiyar kasashen gabashin Afrika, dake karkashin jagorancin shugaban Uganda, Yoweri Museveni.
Sun shawarci kwamitin sulhu game da ganin ko takaka zai tallafawa wannan tawaga ta yadda za a samu zarafin rage tashe-tashen hankali na yanzu a kasar Burundi, in ji mista Gaspar Martins. (Maman Ada)