Hukumar shirya tattaunawar sulhu ta kasar wato CNDI, ita ce kadai ke da ikon shiryawa da kuma jagorantar tattaunawar zaman lafiya a madadin gwamnatin kasar.
A cewar Daniel Gelase Ndabirabe, mai Magana da yawun jam'iyyar mai mulkin kasar, tagawar masu shiga tsakani daga kasar Uganda baza su iya shiryawa da jagorantar tattaunawar sulhun ba, dole ne su samu goyon baya daga hukumar CNDI, da kuma hukumar dake kare muradan Demokaradiyya ta kasar wato CNDD-FDD.
A cewar Ndabirabe, tawagar jami'an na Uganda da kuma CNDI na da babban aiki a gabansu, wajen gabatar da sahinhin tsarin Demokaradiyya ga kasar ta Burundi.
Sai dai kuma Jam'iyya mai mulki a Burundin, ta ce sam ba za ta laminci mutanen da suka kitsa juyin mulki a kasar a ranar 13 ga watan Mayun shekararar 2015 su shiga cikin tattaunawar sulhun ba. (Ahmad Fagam)