An dai dauki wannan mataki ne sakamakon yawaitar hare-haren baya bayan nan da ake kaddamarwa a yankunan Kiunga, da Baragoi, da Milimani, wadanda suka haddasa asarar rayuka da dama.
A cewar wani jami'in rundunar sojin kasar, mahukuntan Kenya sun lura da yadda mayakan kungiyar ta Al-Shabaab ke sauya salon hare-haren su, inda a yanzu suke amfani da ababen fashewa kirar hannu wajen yaki da jami'an tsaro.
A sakamakon hakan, gwamnatin kasar ta kuduri aniyar baiwa 'yan sanda damar amfani da motoci masu sulke, domin taimaka musu gudanar da ayyukan su ba tare da dogaro da rundunar sojin kasar ba.(Saminu Alhassan)