Ofishin bada agajin jin kai na MDD ta bayyana damuwarta game da karuwar harin da ake kai ma ma'aikatan bada agaji a kasar Somaliya wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka guda 17 a bara.
Ofishin ya ce, samun damar bada agajin na daga cikin kalubalen da aka fuskanta a bara a wassu wurare, saboda karuwar rashin tsaro, karancin ababen more rayuwa da kuma kudi.
Ofishin a cikin rahoton da ta fitar na watan Janairu ta ce, a bara kawai an samu fiye da tashin hankali 140 da aka yi kai tsaye a kan kungiyoyin ba da agaji, sannan an samu mutuwar ma'aikatan 17, aka ji ma 18 rauni aka yi garkuwa da 11 sannan aka tsare 38.
A cewar MDD, mutane masu dauke da makamai da ba na gwamnati ba suna cigaba da kasuwanci a wassu yankunan kamar Bakool, BayGedo da Hiraan, don haka suke lalata ayyukan isar da kayayyakin jin kai da manyan ababen bukata na sayarwa ga jama'a a bara.
Ofishin ta kuma ce, samun hanyar isar da kayayyakin jin kai ma har yanzu abun damuwa ne a gundumomi 28 dake kudanci da tsakiyar Somaliyar da kuma gundumar Buuhoodle a arewa.
Duk da cewar akwai cigaba a tattanawar samar da hanyar kaiwa ga wurare kamar Xudur a Bakool, kungiyoyin bada agajin jin kai sun iya kaiwa ga Baidoa a Bay, Bulo Burte a Hiraan, Garbahaarey a Gedo da kuma Wajid a Bakool. Ne kawai ta jirgin sama.
Ofishin bada agajin jin kan na MDD ta kuma bayyana cewar, karuwar matakan rashin tsaro da kuma a wassu lokuta wassu dokokin wajen yana takaita samar da agajin jin kai da kuma lalata ayyukan jin kan.(Fatimah Jibril)