A kwanan baya, ministan harkokin cikin gida na kasar ta Kenya, Joseph Nkaissery ya bayyana cewa, a bara, sakamakon cin gajiyar karuwar karfin yaki da ta'addanci, da amfani da sabbin fasahohi, 'yan sandan Kenya sun murkushe makarkashiyar kungiyar Al-Shabaab ta kai harin ta'addanci a kasar sau da dama. Bayan haka, an ba da labarin cewa, sojojin tsaro na Kenya na kokarin cafke 'yan kungiyar Al-Shabaab dake boye a iyakar kasa tsakanin Kenya da Somaliya.
Masana suna ganin cewa, an riga an sami bambancin ra'ayi a kungiyar, shi ya sa karfinta na tsara kai harin ta'addanci ya ragu. Hakan zai ba da taimako ga Kenya wajen murkushe kungiyar, domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Fatima)