in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 20 sun rasu sakamakon harin ta'addanci da ya auku a Somaliya
2016-01-22 20:28:55 cri
Bisa labarin da aka samu, an ce, a daren ranar alhamis 21 ga wata, an kai harin ta'addanci a wani otel dake arewacin Mogadishu ,babban birnin kasar Somaliya, wanda ya haddasa rasuwar mutane 20, yayin da wasu suka jikkata.

Ana shagalin bikin aure ne a yayin da harin ya auku, kuma akwai mata da yara a cikin wadanda suka rasa rayukansu.

Daga bisani kuma, kungiyar al-Shabaab ta sanar da daukar alhakin tashewar harin.

Bugu da kari, ministan kwantar da kura na kasar Somaliya Abdirisaq Omar ya bayyana cewa, sojojin gwamnatin kasar sun harbe 'yan ta'adda guda hudu, yayin da kama wani shugaban kungiyar, wanda ke da hannu cikin harin ta'addanci da aka yi a babban otel na Mogadishu a shekarar da ta wuce. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China