Somaliya: Al-shabaab ta yi ikirarin kashe sojojin Kenya 100
Mayakan kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya sun yi ikirarin kashe sojojin Kenya 100 a wani harin da suka kai a ranar Jumma'a kan sansanin sojan Kenya dake yankin Gedo, a kudancin Somaliya. A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, kungiyar Al-Shabaab ta kara da cewa mayakanta sun kuma cafke sojojin Kenya da karbe makamai da motocin soja. A cikin harin da suka kai kan sansanin sojan Kenya dake El-Adde, yankin Gedo. Yawan sojojin Kenya da suka halaka a sansanin ya kai 100, a cewar reshen mayakan kungiyar, a cikin wannan sanarwa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku