in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar jami'ar hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD na shirin ziyarartar CAR
2014-02-19 10:10:48 cri

A yau ne ake sa ran babbar jami'ar hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD Valerie Amos, za ta isa Bangui, babban birnin Afirka ta Tsakiya CAR, don kimanta yadda za a taimaka wa yanayin da jama'a ke ciki a Bangui da kuma Bossangoa da ke arewa maso yammacin kasar.

Hukumar kula da harkokin jin kai ta MDD (OCHA) da ke Bangui ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, tana mai cewa, darektan shirin yaki da cutar AIDS na MDD Michel Sidibe da kwamishinar kula da harkokin siyasa ta kungiyar AU, Aicha Laraba Abdullahi na daga cikin wadanda za su rufa mata baya yayin wannan ziyara.

Kasar Afirka ta Tsakuya dai ta tsunduna cikin tashin hankali ne a watan Maris din shekarar 2013, bayan da tsoffin 'yan tawayen Seleka karkashin jagorancin Michel Djotodia suka hau karagar mulkin kasar, wanda daga bisani aka tilasta masa yin murabun a ranar 10 ga watan Janairu.

Alkaluman hukumomin MDD na nuna cewa, tashin hankalin da ya faru a kasar ya tilastawa mutane 714,000 barin gidajensu, ciki har da mutane 288,000 da suka samu mafaka a Bangui, kana rabin mutanen kasar miliyan 4.6 na bukatar agajin gaggawa

Bugu da kari, an yi kiyasin cewa, mutane 15,000 a kasar da ke dauke da cutar sida na karbar maganin rage kaifin cutar, yayin mutane 60,000 suka cancanci samun magani. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China