Kakakin MDD Martin Nesirky, ya ce, rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu UNMISS, ta samu nasarar fidda wasu mutane 33 daga asibitin garin Malakal, zuwa wani babban asibiti domin samun karin kulawar jami'an lafiya.
Hakan dai na zuwa ne bayan wani gumurzun baya bayan nan da ya auku, tsakanin dakarun gwamnatin kasar da na 'yan tawaye a garin na Malakal dake jihar Upper Nile mai arzikin man fetir. Rahotanni sun bayyana cewa, fadan ya janyo kisan sama da mutane 100, da kwasar ganima, tare da kone gine-gine dake garin.
Wani rahoto ma da tawagar ta UNMISS ta fitar a ranar Juma'ar da ta gabata, ya nuna cewa, kimanin mutane 21,500 ne ke samun mafaka a sansaninta dake garin na Malakal. Har wa yau rahoton ya lasafta kisan kiyashi da akewa fararen hula, da azabtar da wasu, tare da yiwa mata fyade, a matsayin wasu daga laifukan da ake zargin bangarorin biyu sun aikata yayin tashe-tashen hankulan dake aukuwa.
Sama da mutane 50,000 ne dai suka rasa matsugunninsu a Sudan ta Kudun, tun bayan barkewar fada a tsakiyar watan Disambar bara, tsakanin dakarun gwamnati masu biyayya ga shugaba Salva Kiir Mayardit, da 'yan tawayen kasar masu goyon bayan korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar. (Saminu)