Wani babban jami'in MDD dake kasar Sudan ya bukaci gwamnatin kasar da jam'iyyar adawa ta SPLM-N a arewacin kasar da su tabbatar sun ba da damar da agajin jin kai zai isa ga jama'a a lokacin da suke halartar tattaunawar sulhu a kasar Habasha.
Jami'in majalissar dake zaune a kasar kuma mai kula da ayyukan jin kai Adnan Khan ya yi maraba da gayyatar da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta mika wa gwamnatin ta Sudan da bangaren adawar ta SPLM-N na arewacin kasar don su tattauna.
Kamar yadda kakakin majalissar Martin Nesirky ya yi wa manema labarai bayani, Mr. Adnan ya ce, akwai matukar bukata ta gaggawa a jihohin kudancin Kordofon da Blue Nile, don haka bai kamata samar da taimakon ceton rayukan jama'a ya zama sharadi a kan cigaban yanayin siyasa ba. (Fatimah)