in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta kudu sun kara wa'adin amincewa da amfani da hanya don kai taimakon jin kai
2016-01-11 09:29:43 cri

Kasashen Sudan da Sudan ta kudu a ranar Lahadin nan suka amince da kara wa'adin yarjejeniyar su ta amfani da hanyar da ta ratsa ta yankin Sudan daga kudanci don kai taimakon jin kai, kamar yadda jaridar kasar Sudan Tribune ta ruwaito.

An ce, Khartoum da Juba sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar bi da kayayyakin agajin jin kai ta yankin kasar Sudan daga kudanci tun a shekara ta 2014.

Yanzu kuma dukkanin bangarorin sun amince da kara wa'adin na wassu watanni 6 daga watan nan na Janairu zuwa karshen watan Yuni, in ji rahoton.

Ali Al-Sadiq, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ya ce, sanin irin karancin abincin da al'ummar kasar Sudan ta kudu ke fuskanta, kasar Sudan ta amince da a isar da kayayyakin agaji zuwa kudanci daga yankin ta.

Ya jaddada burin kasar Sudan na ganin ta rage yawan wahalhalun da al'ummar kasar Sudan ta kudu ke fuskanta, sakamakon tashin hankalin da take ciki.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China