Kasashen Sudan da Sudan ta kudu, sun jaddada aniyar ci gaba da daukar matakan da suka kamata, domin ganin sun warware matsalolin dake addabar su. Wakilan kasashen biyu sun bayyana hakan ne yayin wani zaman tattaunawa da suka gudanar a birnin Khartoum a ranar Lahadi.
Da yake karin haske game da hakan a yayin taron manema labarai na hadin gwiwar wakilan sassan biyu, ministan wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour, ya ce, kasashen biyu sun amince su kyautata dangantakar su, tare da samar da madaidaicin tsarin kiyaye iyakokin su.
Ghandour ya kara da cewa, sun amince da tasirin wanzar da zaman lafiya ga juna. Za kuma su zage damtse wajen tabbatar da wanzuwar sa a kasashen biyu, a wani mataki na tabbatar da cin gajiyar dake tattare da yanayi na lumana ga al'ummunsu.
Shi ma a nasa tsokaci, ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudu Barnaba Benjamin, bayyana muradin kasarsa ya yi, game da aniyar ta ta aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da kasar Sudan, ciki hadda ta wanzar da zaman lafiya da aka daddale a watan Agustan da ya shude.
A watan Satumbar shekarar 2012 ne Sudan da Sudan ta kudu suka amince da muhimmiyar yarjejeniyar hadin gwiwa, karkashin kungiyar IGAD a birnin Addis Ababan kasar Habasha, yarjejeniyar da ta tanaji warware matsalolin tsaro, da na matsayin 'yan kasashe, tare da batun shata kan iyakokin kasashen, da kuma harkokin da suka shafi cinikayya da tattalin arziki. Sai dai kuma yarjejeniyar ba ta warware takaddamar dake tsakanin kasashen biyu game da yankin nan Abyei mai arzikin mai ba, da ma sauran yankunan kan iyakoki da kasashen ke tababa game da matsayin su.(Saminu)