Shugaban Sudan Omar Al-Bashir ya samu rubutaccen sako a ranar Litinin daga takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir kan batun zaman lafiya a Sudan ta Kudu, da kuma huldar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Al-Bashir ya samu wannan sako ta hannun mai ba da shawara a fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu Tot Galwak, a yayin da ya kai ziyara a Khartoum a ranar Litinin.
Sakon ya shafi batun tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, da dangantaka tsakanin kasashen biyu, in ji Galwak a gaban 'yan jarida, bayan ganawarsa da shugaba Al-Bashir.
Takardar ta jaddada niyyar Sudan ta Kudu ta yin shawarwari tare da Sudan kan muhimman batutuwa tsakanin Khartoum da Juba.
Mista Galwak ya bayyana cewa, kasarsa na son ci gaba da raya hulda mai kyau da Sudan domin ganin wadannan kasashe biyu na rayuwa cikin zaman lafiya kuma kusa da kusa.
Jami'in ya nuna yabo game da matsayin da shugaba Al-Bashir ya dauka na nuna goyon baya ga shirin zaman lafiya a kasarsa.
Sudan ta Kudu na fama da yakin basasa tun cikin watan Disamban shekarar 2013, tsakanin dakarun shugaba Kirr da mayakan dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaba kasa Riek Machar.
A makon da ya gabata, Riek Machar, shugaban babbar kungiyar 'yan tawayen Sudan ta Kudu, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar kasashen IGAD ta gabatar tare da sakatare janar na jam'iyyar dake mulki a Sudan ta Kudu, mista Pagan Amum, a birnin Addis Abeba na kasar Habasha. Duk da cewa, shugaba Salva Kiir ya ki ya sanya hannu kan yarjejeniyar tare da neman karin lokaci na makwanni biyu. (Maman Ada)