Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan yayin tattaunawar musamman da ya yi da 'yan jaridu a jiya Laraba, ya ce abun takaici ne a ce dalibai na daukar darasi ta tagar azuzuwansu, saboda karancin kyakkyawan muhallin na karatu.
Ya ce akwai bukatar samar da isassun kayan koyo da koyarwa, da na bincike a dukkanin manyan makarantun dake fadin kasar. Shugaban na Najeriya wanda ya zayyana da dama daga manyan matsalolin dake addabar kasar ta sa, ya ce kamfanonin kasar Sin dake aiki shimfida layin dogo a sassan kasar, za su koma bakin aikin su cikin watanni hudu na shekarar ta 2016, a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar.
Buhari ya kuma bayyana aniyar gwamnatin sa ta kashe makudan kudade don gudanar da manyan ayyuka, musamman a fannin makamashi, da layukan dogo, da hanyoyin mota, da yaki da ta'addanci, tare da samar da guraben ayyukan yi ga 'yan kasa.
Daga nan sai ya jinjinawa kasashen dake nuna sha'awar su ta zuba jari a Najeriya, duk kuwa da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.