A sakon shi na murnar shiga sabuwar shekara ga al'ummar kasar ranar jumma'ar nan, ya ce yana sane cewa 'yan kasar na fuskantar wahalhalun rayuwa a cikin 'yan watannin nan, amma a cewar shi duk na dan lokaci ne saboda gwamnatin shi tana aiki tukuru na ganin 'yan Nigeriya ba tare da la'akari da matsayinsu na zamantakewa ko siyasa ba sun samu sassauci.
Shugaban yayi alkawarin cigaba da yin iyakacin kokarin shi na cika alkawarin da yayi lokacin yakin neman zabe, wanda yace ingantaccen da tabbataccen aiwatar da shirin dake kunshe cikin kasasfin kudin bana zai shawo kan batutuwa da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki da a yanzu haka suke jawo hankalin 'yan kasar.
Daga nan sai ya yaba ma rundunar sojin kasar a kan gaggarumin aikin da suka yi na dakile kungiyar 'yan ta'adda da suka addabi musamman yankin arewa maso gabashin kasar a cikin 'yan shekarun nan. Sai dai ya lura da cewa har yanzu akwai aiki mai yawa da ake bukatar yi a bangaren tsaro.
Dangane da batun cin hanci kuwa, shugaban kasar yace gwamnatin shi zata cigaba da farautar masu hannu a ciki tare da daukan matakan da ya kamata.(Fatimah Jibril)