Shaidun gani da ido sun ce ga alama an dasa bama-baman ne a wani masallaci dake Sulemanti, a yankin Jiddari-Polo a birnin na Maiduguri, kana ababen fashewar sun tarwatse sau biyu a lokacin da jama'a ke shiga masallacin.
Wani jami'in lafiya dake aiki a asibitin kwararru dake birnin na Maiduguri, ya ce an garzaya da gawawwakin mutane 30 zuwa asibitin, sa'an nan wasu 65 na samun jiyyar raunukan da suka samu.
Wannan dai hari ya jefa al'ummar birnin na Maiduguri cikin fargabar sake aukuwar hare-hare makamancin wannan.