in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta zargi sojin saman Sudan da yin ruwan bama bamai a yankinta
2015-06-18 10:07:59 cri

Rundunar sojin kasar Sudan ta Kudu a ranar Laraban nan ta zargi sojin sama na kasar Sudan da yin ruwan bama bamai ta sama a wassu wuraren jihar Upper Nile, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 6, sannan wassu guda 9 suka jikkata, kamar yadda kakakin sojin kasar na Sudan ta Kudu Philip Aguer ya sanar.

Philip Aguer ya ce, sojin saman kasar Sudan sun yi ruwan bama bamai a Panis da Adham na yankin Renk dake jihar Upper Nile, sannan suka sake kai wani harin bama bamai a yankin Maban, duk dai a jihar ta Upper Nile.

A bayanin da ya yi wa kafar yada labarum kasar a ranar Laraba, Philip Aguer ya ce, daga cikin mutane 6 da suka mutu, 4 yara ne kanana, sannan wassu jami'an sojin kasar su 9 sun samu raunuku, yana mai tabbatar da cewa, duk kokarin tuntubar rundunar sojin ta kasar Sudan don jin dalilin wannan ruwan bama bamai a yankin na kasar Sudan ta Kudu bai yiwu ba.

Kakakin sojin daga nan sai ya yi kira ga sojojin Sudan da su daina shiga yankunan kasar Sudan ta Kudu, ya ce, akwai bukatar su yi kokari don a yi aiki tare cikin hadin gwiwwa, a kuma daina tsokanar fadan juna domin a samar da zaman lafiya mai dorewa a kan iyakokin kasashen biyu, da ma al'ummun su baki daya.

Sai dai ba'a samu jin ta bakin bangaren sojin Sudan ba daga bakin kakakin su a kan wannan zargi na Juba.

Sudan da Sudan ta Kudu dai suna musanyar zargin juna a kan goyon bayan kungiyar 'yan tawaye da kasashensu, ganin yadda dukkanin bangarori suka kasa tantance daidai nasu kan iyakar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China