Kamfanin sarrafa albarkatun man fetur na Najeriya NNPC, ya ce matatar sa dake jihar Kaduna ta fara aikin samar da tataccen man fetur har lita miliyan 3.2 a ko wace rana, don biyan bukatun al'ummar kasar da a yanzu haka ke fuskantar karancin man.
A kwanakin baya ne karamin ministan ma'aikatar man ta Najeriya Mr. Emmanuel Kachiku, ya ba da umurnin tura ma'aikatan kamfanin na NNPC zuwa tasoshin samar da man fetur dake sassan kasar daban-daban, domin sa ido ga aikin samar da man fetur, ta yadda za a dakile matsalar karancin man yadda ya kamata.
A cewar Mr. Kachiku, Najeriya na da isashen man fetur, kana ya yi kira ga masu tuka motoci da kada su damu game da halin da ake ciki, ya ce boyewa da fasakwaurin man ya sabawa dokar kasar. (Amina)