Shugaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki shi ne ya bayyana hakan a kwaryar majalisar bayan da ya karanta sunayen ministocin a karon farko, makonni biyu tun bayan da aka mikawa majalisar takardar sunayen a hukumance. Matakin da ya kawo karshen rade-raden da jama'a ke yi game da rashin bayyana ministocin na tsawon watanni.
Daga cikin sunayen ministocin da shugaban majalisar dattawan ya karanta, har da tsoffin gwamnoni biyar, tsofon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya,kakakin jam'iyyar APC mai mulki da kuma manajan darektan kamfanin mai na kasar.
A ranar 30 ga watan Satumba ne shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa majalisar dattawan kasar kashi na farko na sunayen ministoci 21 daga cikin a kalla sunaye 36 da ake fatan nadawa a wannan mukami domin ta tantance.(Ibrahim)