Muhammadu Buhari ya fadi hakan ne a garin Dutse na jihar Jigawa lokacin da ya je bikin kaddamar babban taron shekara ta 2015 na hafsan rundunar sojin kasar.
Ya jaddada cewa, lokacin da aka diba zai iya zama wani jagora, kuma idan ayyukan da ake yi na kawo karshen ta'addanci a duk fadin kasar na bukatar karin lokacin, gwamnatin tarayya ba za ta yi jinkirin ganin ta kara ba domin a samu shawo kan duk wani abin da zai nemi kunno kai a kasar.
Shugaba Buhari wanda babban hafsan rundunar tsaron kasar Janar Gabriel Olonisakin ya wakilta ya yi bayanin cewa, sojojin kasar dole ne su samar da dabarun da za su kawo karshen kalubalen da ke fuskantar kasarsu, kuma tabbatar da kawo karshen harin 'yan kungiyar ta ko wane hali.
Muhammadu Buhari ya sanar wa mahalarta taron cewa, gwamnati za ta duba halin da ake ciki a yanzu, sannan ta dauki matakin da ya dace domin ganin an dakile kungiyar 'yan ta'adda a kasar baki daya.(Fatimah)