in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin ya samar da kayayyakin tallafi a arewacin Najeriya
2015-10-20 13:15:15 cri

 

A kwanakin baya, kamfanin CGCOC na kasar Sin dake Najeriya ya samar da kayayyakin tallafi da dama ga jihar Zamfara dake arewacin kasar wacce ke fama da bala'in ambaliyar ruwa.

Bayan da aka shiga lokacin daminar bana, an samun ruwa a wurare daban daban a Najeriya, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa. Jihar Zamfara na da koguna da dama, don haka an gamu da bala'in a wasu yankunan jihar, har ma an lalata gidaje da hanyoyin mota da dama. Da zarar kamfanin CGCOC na kasar Sin ya samu labarin, nan take ya samar da kayayyakin tallafi ga jihar Zamfara don taimakawa mutanen da bala'in ambaliyar ruwan ya shafa.

A gun bikin mika kayayyakin, wani jami'in gwamnatin jihar Zamfara ya yi bayani kan halin da ake ciki a jihar, a madadin gwamnan jihar da jama'ar jihar, inda ya nuna godiya ga kamfanin na CGCOC. Sannan ya mika kayayyakin ga shugaban hukumar kula da shirin ko-ta-kwana na jihar, tare da umarce shi da a rarraba kayayyakin cikin hanzari ga mutanen da bala'in ya shafa.

Masu bada ceto na kamfanin CGCOC sun bayyana cewa, za su yi iyakacin kokarinsu wajen taimakawa jama'ar da bala'in ya shafa, kuma suna fatan jama'ar za su sake gina gidajensu da farfado da rayuwarsu cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China