Darektan dake jagorantar wadannan ayyuka James Ole Serian, ya bayyana cewa makaman da aka boye an gano su ne a dajin Boni na yankin Panda Nguo na Lamu, dake kusa da iyaka tsakanin Kenya da Somaliya.
Mista Ole Serian ya bayyana cewa yanzu suna bincike kan wadannan makamai ko kungiyar Al-Shabaab ta wuce da su ne ta hanyar sumogal domin yin amfani da su wajen kai hare-hare, ko kuma wadannan makamai su ne aka yi amfani da su wajen kai hare haren ta'addanci na baya bayan nan a Lamu.
Panda Nguo na daya daga cikin wuraren da aka kashe mutane fiye da 100 a cikin kwanaki uku a lokacin hare-haren Al-Shabaab a shekarar da ta gabata a yankin Lamu.
Mista Ole Serian ya nuna cewa bandigogi samfurin 302 guda biyar da manyan bindigogi tare da harsasai guda 27 an mika su domin yin bincike kansu, tare da jaddada cewa jami'an tsaro za su tsaye dajin Boni har zuwa wani lokaci. (Maman Ada)