Shugaba Kenyatta ya yi wannan kiran ne a lokacin bikin yaye kananan hafsoshi da ya gudana a yankin Nakuru. Yana mai cewa, makomar kasar ya rataya ne ga yadda al'umma ta samu ingantaccen tsaro,zaman lafiya, shugabanci na gari da manufofin bunkasa tattalin arziki.
Shugaban na Kenya ya ce, sojoji su kadai ba za su iya kawar da 'yan ta'adda ba, don haka ya yi kira ga daukacin 'yan kasa masu kishi, da su hada kai don ganin bayan wadannan mahara.
Ya kuma yi kira ga kananan hafsoshin da aka yaye, da su kasance masu nuna abin misali na gari ta yadda sauran jama'a za su yi koyi da su.
Shugaba Kenyatta ya kuma bayyana kudurin gwamnati na samar da kayan aikin zamani ga jami'an tsaron kasar ta yadda za su dace da yanayin tsaron da ake ciki.
Masana harkar tsaro dai na ganin cewa, yanzu haka an samu gagarumin canji a kasar ta Kenya, ganin yadda jama'a ke kara sanya ido kan mutanen da ba su yarda da su ba, tare da kai rahoto ga 'yan sanda. Haka zalika, su ma 'yan sanda sun kara samun karewa wajen tafiyar da ayyukansu.
Kananan hafsoshin da aka yaye a bikin na jiya Alhamis sun fito ne daga kasashen Tanzaniya,Rwanda,Uganda da kuma Burundi. (Ibrahim)