Babban sakatare na ma'aikatar kula da kamfanoni da cigaban masana'antun kasar Adan Mohamed, shi ne ya tabbatar da hakan yayin wani taro kan al'amurran masana'antu a birnin Nairobi, ya ce kasar Kenya, ta gamsu da irin gudumowar da kamfanonin kasashen wajen ke bayarwa wajen habaka tattalin arzikin kasar, don haka gwamntin kasar ta sha alwashin samar da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari daga kasashen waje.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar tuni ya sanya hannu na amincewa da dokar masana'antun tun a watan Satumba. Dokar wadda a halin yanzu ba ta fara aiki gadan gadan ba, amm ana sa ran idan dokar ta fara aiki, zata maye tsarin da ake amfani da shi wajen rigistar kamfanoni a kasar shekaru 50 da suka gabata.
Ana sa ran idan sabuwar dokar ta fara aiki, kamfanonin 'yan kasashen waje da suka kafa rassa a Kenya, za su ware kashi 30 cikin 100 ne kachal na ikon mallakar kamfanonin ga kasar ta Kenya.(Ahmad)