A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da asusun din ya yi tare da jami'an gwamnatin Rwanda a birnin Kigali, Laure Redifer, babbar jami'a ta IMF, ta jaddada cewa faduwar man fetur a kasuwannin duniya da kuma hasashen ja da bayan bunkasuwa a cikin muhimman kasuwanin fitar da kayayyaki na Rwanda, da ma tuni bangaren hakar ma'adinai yake ji a jiki, zai shafi bakin gwargwado karfin fitar da kayayyakin Rwanda a cikin tsawon gajeren lokaci. (Maman Ada)