Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a yayin bikin bude taron baje kolin harkokin samar da sinadaran kare tsirrai, da harkokin cinikayyar amfanin gona ko CAC a takaice, wanda aka bude ranar Talata a gundumar Nakuru dake kasar ta Kenya, ya kara da cewa Sin na da kwarewa a fannin noma na zamani, da fannin samar da sinadaran kare amfanin gona, don haka take fatan gudanar da hadin gwiwa da Kenya a wannan fanni.
Ya ce ya dace mahalarta dandalin na wannan karo daga kasashen biyu, su yi amfani da wannan dama wajen karfafa hadin kansu, domin cin gajiyar sabbin fasahohin noma, da kuma kirkire-kirkiren dake taimakawa wannan muhimmiyar sana'a. (Saminu)