Yayin ganawar tasu a nan birnin Beijing, Li ya bayyana cewa, a halin da ake ciki, ana ci gaba da bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Liberiya cikin kyakkyawan yanayi, ana kuma samun babban ci gaba a fannin hadin gwiwar sassan biyu.
Ya ce Sin na fatan kara sada zumunci da Liberiya, tare da zurfafa hadin gwiwa a fannonin fitar da albarkatu, da samar da manyan ababen more rayuwa ga jama'a da dai sauransu. Kaza lika Sin za ta ci gaba da taimakawa Liberiya a fannin samar da ci gaba da rage talauci, da zummar cimma moriyar juna.
A nata bangare, shugaba Sirleaf cewa ta yi, yayin da jama'ar kasar Liberiya ke fama da cutar Ebola, Sin ta samar da taimakon gaggawa gare ta, wanda hakan ya jawo hankulan duniya, ya kuma janyi taimakon kasa da kasa. Ta ce, Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kara azama ga Liberiya wajen samun nasarar shawo kan cutar Ebola.
Baya ga hakan, kasashen biyu na sada zumunci tsakaninsu cikin dogon lokaci, sun kuma samu ci gaba matuka a fannin hadin gwiwa tsakaninsu. A cewar shugaba Sirleaf, gwamnatin kasar ta na dora muhimmanci ainun ga dangantaka tsakanin ta da Sin, tana kuma godiya ga taimakon da gwamnatin Sin ta bayar a fannin samun ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar Liberiya.
Ta ce a yanzu haka Liberiya na kan wani muhimmin lokaci na farfadowa, da bunkasuwa, a sabili da haka, take fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin, matakin da ya zamo abin koyi a fannin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka da Sin.
A wannan rana kuma, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Zhang Dejiang ya gana da shugaba Sirleaf a birnin Beijing.(Fatima)