Wadannan rukuni su ne na farko cikin rukuni 18 na ma'aikatan kiyaye zaman lafiya daga kasar Sin da suka fara aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Liberiya tun daga shekara ta 2003 a karkashin bukatar kwamitin tsaro na MDD mai doka ta 1509.
Wani rukunin zai tashi zuwa Liberiyan a ranar 17 ga watan nan. Wanda gaba daya rukunin biyu suka kunshi ma'aikata 508 a ciki akwai sojojin bangaren injiniya 275, bangaren sufuri 190 da kuma bangaren kiwon lafiya 43.
Aikin su ya hada da samar da ababen more rayuwa kamar yin hanyoyi da gadoji, gyara a gidajen zama da kuma filin saukan jiragen sama sannan da daidaita ababen samar da ruwan sha da wutan lantarki.
Rukunin har ila yau suna da alhakin jigilar ma'aikata da kayayyakin aiki, samar da ayyukan jinya, bada kariya daga cututtuka da ake saurin dauka da kuma bada kariya tare da magance barkewar annoba. (Fatimah)