A yau da safe ne Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya yi shawarwari da shugabar gwamnatin kasar Jamus madam Angela Dorothea Merkel a nan Beijing.
A yayin shawarwarin, Li Keqiang ya ce, bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Jamus tana taimakawa wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai, yayin da ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Turai ke taimakawa wajen bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Jamus.
Sin na fatan Jamus, kasancewarta muhimmmiyar mamban kungiyar Tarayyar Turai, za ta kara azama kan yin shawarwari a tsakanin kasashen Sin da Turai kan yarjejeniyar zuba jari, nazarin yiwuwar kafa yankin ciniki maras shinge a tsakanin kasashen Sin da Turai da dai sauransu, a kokarin samun sakamako cikin hanzari da kuma kawo wa jama'a alheri.
A nata bangaren kuma, madam Merkel ta ce, bisa kyakkyawan tushen da kasashen 2 suka kafa yanzu, Jamus na son inganta yin mu'amala a matakai daban daban na kasashen 2, habaka hadin gwiwa da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannin kirkire-kirkire, bullo da sabbin fannonin yin hadin gwiwa, kara yin mu'amala a tsakanin kananan hukumomi, tare da shirya shekarar yin mu'amala a tsakanin matasan kasashen 2 a shekara mai zuwa, a kokarin sa kaimi kan bunkasa dangantaka a tsakanin Jamus da Sin.
Bayan shawarwarin, Li Keqiang, da madam Merkel sun gana da manema labaru tare, inda a cewar Li Keqiang, kasashen 2 sun yarda da ci gaba da yin mu'amala a tsakanin manyan jami'ansu, kyautata tsare-tsare a matakai da sassa daban daban a kokarin inganta fahimta da amincewa da juna sakamakon yin tattaunawa da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2. Madam Merkel ta ce, Jamus na da imani kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Yadda kasar Sin take kara kokarin sauya hanyoyin raya tattalin arziki da kuma bunkasuwar kasar mai dorewa zai taimakawa wajen samar da sabuwar damar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2. (Tasallah Yuan)