Kasashen Afrika 8 dake amfani da harshen faransanci na halartar taron DecNet karo na 13, da ya kasance wani dandalin musanya da daukar darasi kan batutuwan baiwa yankuna ikon tafiyar da harkokinsu a Afrika, gudunmuwar haraji na cikin gida ga ci gaban tattalin arziki, da aka bude a ranar Talata a birnin Lome na kasar Togo.
Dandalin ya hada abokan hulda da kwararru na tsare tsaren GIZ, cibiyar huldar dangantakar kasa da kasa ta Jamus, masu ruwa da tsaki na cikin gida na shirin baiwa yankuna ikon tafiyar da harkokinsu na kasashen Benin, Burkina Faso, Burundi, Madagascar, Mauritania, Mali, Nijar da kuma Togo.
Haduwar ta kwanaki hudu, na bisa taken "haraji na cikin gida a cikin ayyukan yankunan kasa" na da manufar ba da gudunmuwar da ta dace ga harkokin haraji wajen kokarin ci gaban kasashen Afrika.
Haka kuma zai bullo da hanyoyin da za su taimaka wa yankunan kasa tanadar dabarun da za su iya taimaka musu wajen kyautata matsalolinsu na kudi, da ingiza tafiyar da harkokin mulki na cikin gida a wadannan kasashe.
Mahalarta taron za su nazari kan wata hadakar siyasa ta cikin gida da shiyya da za ta kai al'ummomi da yankuna na cikin gida ba da wata gundunmuwar haraji da za ta kawo ci gaba, in ji madam Awa Gueye Thioune, wakiliyar sakataren din din din na DecNet.
A cewar madam Thioune, kasashen Afrika suna da matsaloli wajen bunkasa ci gaba na cikin gida, kuma yana da kyau ganin hukumomi na cikin gida sun karbi wannan tafiya domin amsa karin bukatun jama'a cikin lokaci, bisa dogaro da wani tsarin haraji na cikin gida na gaskiya da adalci, bisa amincewa kuma mai nagarta. (Maman Ada)