Bunkasuwar kayayyakin da ake sarrafawa cikin gida GDP na Afrika zai dore a shekarar 2015 da shekarar 2016, da kashi 4,5 cikin 100 da kuma kashi 5 cikin 100, bayan shekaru biyu na matsakaiciyar karuwa wato kashi 5 cikin 100 a shekarar 2013 da kuma kashi 3,9 cikin 100 a shekarar 2014, a cewar wani rahoton da aka fitar a ranar Litinin.
Wannan rahoto mai taken "makomar tattalin arziki a nahiyar Afrika a shekarar 2015", an shirya shi cikin hadin gwiwa tsakanin bankin ci gaban Afrika na ADB, cibiyar ci gaba ta OECD da kuma tsarin ci gaba na MDD wato PNUD.
A cewar rahoton, karfin tattalin arzikin Afrika ya tare a shekarar 2014. Yammacin Afrika ya samu bunkasuwar tattalin arziki bakin gwargwado da kashi 6 cikin 100 a shekarar 2014, duk da cewa ya yi fama da cutar Ebola, a yayin da bunkasuwar yankin kudancin nahiyar Afrika ta tsaya kan kashi 3 cikin 100, kuma karuwar ci gaban tattalin arzikin Afrika ta Kudu ta tsaya ga kashi 1,5 cikin 100 kawai.
Yawan hanyoyin samun tallafi ga tattalin arzikin Afrika na ci gaba da karuwa. Bangaren kwangiloli, sauran bangarori kamar noma, masana'antun harkar ma'adinai, gine gine da sauran ayyuka su ne muhimmman ginshikan karuwar tattalin arziki.
Haka kuma ta wani bangare, zuba jarin kai tsaye na waje (IDE) a Afrika zai cimma dalar Amurka biliyan 73,5 a shekarar 2015, dalilin karuwar jarin kasar Sin a cikin sabbin ayyuka, a cewar wannan rahoto, dake kara nuna cewa, kasar Sin za ta cigaba da kasancewa babbar abokiyar huldar kasuwanci ta Afrika bayan tarayyar Turai. (Maman Ada)