in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guinea, Liberiya da Saliyo sun cimma wasu hanyoyin ingiza tattalin arziki
2015-06-29 09:59:49 cri

Shugabannin kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo sun cimma a ranar Lahadi a Conakry da wasu hanyoyi, tare da kebe kudaden shirin shiyya na ingiza tattalin arzki domin ingiza tattalin arziki, tun bayan annobar Ebola.

A yayin taron da suka gudanar a hedkwatar kasar Guinea bisa tsarin taron gaggawa na kungiyar kasashen kogin Mano, shugaban kasar Guinea Alpha Conde, da takwarorinsa na Saliyo Ernest Bai Koroma da Ellen Johnson Sirleaf ta Liberiya, tare da ministan harkokin wajen kasar Cote d'Ivoire Charles Koffi Diby, da ke wakiltar shugaban kasar Cote d'Ivoire, sun tattauna wasu kudurori da dama da ke da nasaba da tsarin dokoki da kudi, ta yadda za'a aiwatar da shirin baki daya da dorewa na tsare tsaren mai do ci gaban tattalin arziki da na jama'a, tun bayan annobar Ebola.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron, shugabannin kasashen hudu sun amince da yin la'akari da fannoni da dama na kudi da za'a mika ga kungiyoyin ba da lamuni na duniya.

Shirin farko na tsarin shiyya, ya tasan ma dalar Amurka biliyan 1,76, kuma ya shafi kiwon lafiya, ruwa, tsabta, zaman lafiya, noma, tsaron abinci da tsarin tallafawa bangaren masu zaman kansu.

Shirin na biyu ya shafi shimfida hanyar motoci, samar da makamashi, fasahohin zamani da sadarwa bisa kudin da suka cimma dalar Amurka biliyan 2,24. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China