Hasashen masana na nuna cewa, tattalin arzikin yankin dake kudancin Saharar Afirka, zai kara fuskantar koma baya, sakamakon karyewar farashin hajoji, da faduwar darajar kudaden kasashen yankin, tare da karancin bukatar hajojinsu a kasuwannin waje.
Wani rahoto da cibiyar nazarin tattalin arziki ta BMI dake Birtaniya ta fitar, ya nuna cewa, cikin shekaru 5 masu zuwa, yanayin tattalin arzikin duniya ba zai yiwa yankin kudu da hamadar Sahara dadi ba, idan an kwatanta da tagomashin da yankin ya samu a shekaru 5 da suka gabata.
Rahoton binciken ya nuna cewa, cikin shekaru 5 masu zuwa, karyewar darajar kayayyaki, da kuma karancin bukatun hajoji a kasuwannin duniya za su kara ta'azzara, wanda hakan zai yi matukar shafar ci gaban yankin.
Duk dai da wannan hasashe, cibiyar ta BMI ta ce, akwai kasashe 10 daga yankin, wadanda za su samu saurin bunkasuwa bisa ma'aunin GDP. Wadannan kasashe kuwa su ne Burkina Faso, da Congo, da Cote d'Ivoire, da kuma Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Sauran su ne kasar Habasha, da Kenya, da Mozambique, da Rwanda, da Tanzania da kuma Zambia.
Rahoton ya ce, manyan dalilan da za su baiwa wadannan kasashe damar samun ci gaba, sun hada da faduwar darajar mai, wanda zai share fagen daukakar sauran sassan tattalin arziki, sai kuma bunkasar sha'anin hakar ma'adanai, da fadadar kasuwanni, tare da manufofin gwamnatoci dake da matukar tasiri ga samar da ci gaba.
Kaza lika rahoton ya ce, kasashe irin su Najeriya za su fuskanci koma baya, kasancewar mai yiwuwa ta fita daga jerin kasashe 10 mafiya saurin bunkasuwa, sakamakon karyewar farashin mai, wanda shi ne jigon tattalin arzikinta, yayin da kuma kasar Ghana za ta fuskanci kalubale, sakamakon dalilai na cikin gida, da suka hada da karancin wutar lantarki da dai sauransu. (Saminu)