Mr. Ruto wanda ya bayyana hakan ga taron dandalin shiyyar a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. Ya ce, muddin nahiyar tana fatan samun 'yancin siyasa da tattalin arziki, wajibi ne ta kawar da batun nuna bambancin kabila, addini da kuma asali.
Mr. Ruto ya kuma yi kira ga shugabannin nahiyar da su canja yadda ake kallon nahiyar a matsayin wadda talauci da cin hanci da cututtula suka yiwa katutu.Yana mai cewa.lokaci ya yi da al'ummar Afirka za su kalli kansu su bayyanawa duniya yadda nahiyar ta ke a zahiri.
Mataimakin shugaban kasar ta Kenya ya kuma ce, Afirka tana bukatar wata sabuwar alkiblar nuna kisan kasa wadda za ta yaki barazanar da sauran kasashen nahiyar ke fuskanta, shigo da sabbin masana'antu, fasahohin kere-kere da Internet wadanda za su taimakawa wajen magance kalubalen da nahiyar ke fuskanta.
A farkon wannan shekara ce dai kasashen na Afirka suka sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwar bai daya, da nufin magance matsalar zirga-zirgar mutane da kayayyakin tsakanin kasashen nasu.(Ibrahim)