A yayin taron na yini 3, an tattauna batutuwan da suka shafi yaki da ta'addanci, da hana masu tsattsauran ra'ayin addini jan ra'ayin mutane, da inganta hadin gwiwa a fannin tsaro a shiyya-shiyya. Jami'ai da kwararru a harkokin tsaro, da malaman addini, da wakilan kungiyoyin jama'a sama da 300 daga kasashe sama da 40 ne suka halarci taron.
A gun bikin bude taron, mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto, ya ce yanzu haka kasar Kenya na fuskantar kalubalen tsaro kamar tashe-tashen hankali da hare-haren ta'addanci.
Ya ce, a kwanan baya, ya yin wani hari da kungiyar Al-shabab ta Somaliya ta kai a Kenya, baya ga kasancewar maharan sun hada da matasan kasar ta Kenya, a daya hannun kuma wasun su sun fito ne daga kasashen Turai. Sabo da haka, ya ce ya kamata kasashen duniya su inganta hadin gwiwa wajen hana masu tsattsauran ra'ayi zuga matasa da jan ra'ayin su domin ta da zaune-tsaye.
Shi ma a nasa jawabi, minista mai kula da harkokin cikin gidan kasar ta Kenya Joseph Nkaissery, kira ya yi ga kasashen duniya da su kara ba da gudummawa, a fannin ayyukan wanzar da zaman lafiya a Somaliya, domin kawar da hare-haren kungiyar Al Shabab. (Bako)