Kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da harkokinsu a kasar Afirka ta Kudu sun nanata kudurinsu na ganin bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka.
Wakilan kamfanonin harhada motoci na FAW, reshen kasar Afirka ta Kudu, da kuma kamfanin cinikayya ta hanyoyin zamani wato UnionPay ne suka bayyana hakan a lokacin da suke jawabi a wani dandalin tattaunawa game da hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
Wakilan kamfanoni sun bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na daukar Afirka a matsayin aminiyar da ke son kulla dangantakar mahdi ka ture da nahiyar. Bugu da kari kasar Sin ba ta yiwa nahiyar katsalanda kan harkokin na siyasa ko tilastawa jama'arta shugabannin da za su zaba ko cusa musu wani ra'ayi ko akida ba.
Sun kara bayyana cewa, kasar Sin tana gudanar da ayyukan da nahiyar da kuma al'ummominsu za su dauki shekaru masu tarin yawa suna amfana, sabanin kasar Amurka da Turai da ke mayar da hankali kan ayyuka na gajeren lokaci.
Jami'an sun bayyana cewa, akwai tarin darussa da nahiyar za ta iya koyo daga kasar Sin wadanda za su taimakawa ci gaba al'ummomi da kuma tattalin arzikinsu.
Sun kuma kammala da cewa, Afirka da tauraruwar ke haskakawa a halin yanzu, tana bukatar kasa kamar Sin wadda ke da burin inganta kayayyakinta na more rayuwa.(Ibrahim)